Taron jam’iyar da ke mulki ANC da aka fara jiya lahadi, za a kwashe kwanaki uku ana yi a birnin Pretoria.
Wasu ‘Ya‘yan jam’iyyar sun bukaci shugaban kasar ne da ya sauka tun bayan matakin koran Ministan kudi na kasar Pravin Gordhan wanda ake kallon yana da kima a idanun jama’a.
Majiyoyi daga dakin taron na cewa an yi ta yunkurin tsige shugaban kasar a taron da aka fara amma kuma Shugaban Jam’iyyar ya yi uwa ya yi makarbiya wajen hana daukan matakin.
Sakataren Jamiyyar ta ANC Gwede Mantashe ya shaidawa manema labarai a wajen taron cewa taron ya yi armashi ganin babu wani mummunan abinda ya faru.